IQNA

Wani Dan Takarar Shugabancin Amurka Ya Sake Yin Batunci Ga Musulmi

16:50 - February 17, 2016
1
Lambar Labari: 3480150
Bangaren kasa da kasa, Ben Karsen daya daga cikin yan takarar da suka fito suna neman cancantar tsayawa takarar neman shugabancin Amurka ya bayyana musulmin da suke cewa za su bi shari’ar muslunci a kasar a matsayin masu matsalar hankali.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na WND cewa, a wata zantawa ta tashar talabijin da ya gudanar, Karsen ya bayyana cewa musulmin da suke zaunea kasar Amurka da suke tunanin kafa shari’ar musulunci suna fama da matsalar tabuwar kwakwalwa.

Wannan mutum wanda tsohon likita ne ya bayyana cewa; mutumin da yake da matsala irin wannan ne kawai zai iya gazgata abin da irin wadannan musulmi suke fada.

Ya ci gaba da cewa kasar Amurka kasa ce wadda ba ta musulmi ba, akan haka musulmi su daina mafarkin cewa za su iya mayar da wannan kasa tasu kuma mallakinsu.

Wannan dai bas hi karon farko da musulmi suke fusknatr irin wannan cin zarafi daga masu neman kujerar takarar shugabancin kasar Amurka ba.

Ko a lokutan baya wani daya daga cikin yan takara da wanann jam’iyya ta masu tsatsauran ra’ayi ya irin wannan furuci domin kaskantar musulmi.

Kiyayya da musulmi na ci gaba da karuwa a tsakanin al’ummar kasar Amurka, musamman a cikin wadannan lokuta da ayyukan ta’addanci ke ta kara samun wurin zama tare da taimakon kasashen turai da kasashe masu akidar kafirta musulmi.

3476349

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 3
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Duk woni kowota wodanda ke bata indinin musulunci allah ya.isa
captcha