IQNA

Tarayyar Turai Ta Fitar Da kudiri Kan Wajabcin kawo Karshen Zalunci Kan Rohingya

22:27 - December 15, 2017
Lambar Labari: 3482203
Bangaren kasa da kasa, babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta ce Kungiyar EU za ta taimakawa musulmin Rohinga na kasar Myanmar da suke gudun hijra a Bangladesh.

Kamfanin dillancin labaran kasar Jamus ya nakalto Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini a birnin Strasbourg na cewa a kwai bukatar kudi da taimako na gaskiya domin taimakawa musulmin Rohinga da suke gudun hijra su koma kasar su da gaggauwa.

Mogherini ta ce kungiyar tarayyar Turai za ta taimaka daidai iyawarta ga wadanda suke son komawa gida daga cikin al'ummar musulmin Rohinga dake hijra a Bangladesh su koma kasarsu.

Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai ta kara da cewa kungiyoyin bayar da agajin gaggauwa dake jihar Rakhine sun tabbatar da cewa suna iya karbar mutane har dubu dari biyar cikin musulmin Rohingar da suke yi hijra a Bangladesh.

Tun a shekarar dubu biyu da sha biyu ne dai musulmin Rohinga su ke fuskantar kisa da azabtarwa da kona gidajensu da dukiyarsu a hannun sojoji da yansanda da kuma masu tsattsauran ra'ayin addinin Buddha, irin wannan cin mutunci ya sake tasowa a karshen watan Augusta na shekarar dubu biyu da sha bakawai da muke ciki.

3672792

 

 

 

captcha