IQNA

Kwamitin Tsaro Zai Duba Daftarin Kudiri A Kan Batun Matakin Trump A Kan Quds

22:36 - December 17, 2017
Lambar Labari: 3482210
Bangaren kasa da kasa, Kwamitin Tsaron MDD ya fara gudanar da bincike kan koken da kasar Masar ta shigar na watsi da sabon kudirin shugaban kasar Amurka Donald Trump kan birnin Qudus.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya Asabar mambobi 15 na kwamitin tsaron MDD suka fara gudanar da bincike a game da koken da kasar Masar ta gabatar na watsi da sabon matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin hedkwatar Haramtacciyar kasar Isra'ila.

Rahoton ya ce akwai yiwuwar cewa a ranar Litinin ko Talata na wannan mako da muke ciki, za a kada kuri'ar watsi da wannan kuduri, duk kuwa da cewa kudirin nada magoya baya a tsakanin manbobin kwamitin tsaron MDD, kuma akwai yiwuwar Amurka ta hau kujerar naki a game da wannan kudiri.

Cikin koken da Masar ta gabatar, duk wani kudiri da zai canza yanayin birnin Qudus da al'ummarsa, ba shi da wani tasiri a hukumance, kuma bisa dokokin MDD wajibi ne ayi watsi da shi,sannan kuma an bukaci kasashen duniya da su kauracewa matakin Amurka na mayar da Ofishin jakadancinsu a Haramtacciyar kasar Isra'ila zuwa birnin Qudus.

A ranar 6 ga watan Disamba da muke ciki ne, duk da irin adawar da kasashen Duniya suka nuna, Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ayyana Birnin Qudus a matsayin hedkwatar Haramtacciyar kasar Isra'ila tare da bada umarnin dauke ofishin jakadancin kasarsa daga birnin Tel-Aviv domin mayar da shi zuwa birnin Qudus.

3673297

 

 

captcha