IQNA

Cibiyar Azhar Ta Fitar Da Wani Gajerin Fim A Cikin Harshen Turanci Kan Jihadi A Musulunci

23:37 - March 15, 2018
Lambar Labari: 3482476
Bangaren kasa da kasa, cibiyar musulunci ta Azhar a kasar Masar ta fitar da wani kajerin im da ta shirya a cikin harshen turanci kan matsayin jihadia  cikin addini mslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadal Balad cewa, Azhar ta fitar faifan bidiyon ne mai taken The Concept of Jihad, da nufin gyara tunanin masu bata sunan addinin muslunci da sunan suna jihadi.

A cikin fim din an bayyana ma’anar jihadi da kuma hikimarsa a mahangar addinin muslunci, da kuma dalilan da suke sanya wa a yi shi da kuma wadanda ake yin shi a kansu.

Fim din ya nuna cewa jihadi a musulunci yana zuwa ne a matsayin kare kai daga wadanda suka yi shishigi a kansu musulmi ko kuma suke da nufin cutar da musulmi, kuma ko a hakan ma yana da sharudda wadanda sai an cika su ne ake kaddamar da shi.

Wannan dai yana daga cikin shirin da cibiyar Azhar ta fara aiwatarwa ne na neman yin gyara dangane da aidar takfiriyya da ke gurbata akida musulunci da kuma bata sunan musulunci a idon duniya, inda suke aikata ta’addanci da sunan jihadi a musulunci.

3699852

 

 

 

 

captcha