IQNA

An Bude Gasar Kur'ani Ta Kasa Da Kasa A Masar

22:42 - March 17, 2018
Lambar Labari: 3482481
Bangaren kasa da kasa, An bude gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a lardin Portsaid na kasar Masar tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashen ketare.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na jaridar yaum sabi ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da taron bude gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa ne a lardin na Portsaid, tare da gabtar da jawabai daga manyan malaman addini na kasar da suka halarci bukin bude gasar.

A lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron, gwamnan lardin Portsaid Adel Gadban, ya bayyana cewa hakika wannan gasa wadda irinta ce ta farko wadda ta kebanci kasashen larabawa zalla tana da matukar muhimmanci, kasantuwar hakan zai kara karfafa gwiwar matasa larabawa domin komawa zuwa lamarin kur'ani.

Baya ga hakan wasu daga cikin manyan malamai daga ciki da wajen kasar ta Masar da suka halarci wurin sun gabatar da jawabai da aka watsa kai tsaye a tashoshin yada labarai na kasar ta Masar.

3700487

 

captcha