Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na vetogate.con cewa, wadannan matasa musulmi suna halartar dukkanin tarukan gasar da Azhar ta shirya a birane daban-daban na kasar Masar.
Ahmad Junaid shugaban cibiyar shirya gasar kur'ani mai tsarki a jami'ar Azhar ya bayyana a yayin ganawa da wadannan matasa cewa, abin farin ciki ne yadda lamarin kur'ani yake kara samun wurin zama a tsakanin matasa musulmi na Rasha.
Ya kara karfafa gwiwarsu wajen ci gaba da kara bayar da himma wajen lamarin kur'ani da kuma karfafa harshen larabci.