IQNA

Gasar Rubutu Kan Bincike A Cikin Kur’ani Da Sunnah A Cibiyar Azhar

22:36 - March 20, 2018
Lambar Labari: 3482493
Bangaren kasa da kasa, an bude rijistar sunayen masu bukatar shigar gasar mata zalla ta bincike a cikin ayoyin kur’ani da sunnar manzo karkashin cibiyar Azhar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadal Balad cewa, an fara rijistar sunayen masu bukatar shigar gasar mata zalla ta bincike a cikin ayoyin kur’ani da sunnar manzo (ASW) bisa kulawar cibiyar Azhar da ke kasar Masar.

Wannan gasa dai tana daga cikin irinta akan gudana kan batutuwa daban-daban na ilimi, inda akan rubutu kan wani maud ui daga bisani kuma a buga wanda ya zo na daya.

Gasar wadda ta shafi mata zalla ce, za ta yi bincike kan wani maudui ne a cikin kur’ani ko sunnar manzo, tare kawo bayani da ya shafi wannan maudui da kuma fitar da muhimman abubuwan da ya kamata a sani kan hakan.

Gasar dai bisa kaida ba ta wuce shafi 100 zuwa 200, kuma daga bisani za a rubuta a bin da makalar ta kunsa a cikin shafuka 10 zuwa 20, kuma wa’adin mika gasar zai kasance daga nan zuwa Disamban karshen wannan shekara.

3701404

 

 

 

captcha