IQNA

Wasu Mahara Sun Kai A Wani Masallaci A Afirka Ta Kudu

23:57 - June 14, 2018
Lambar Labari: 3482758
Bangaren kasa da kasa, Wasu mahara sun kai farmaki cikin wani Masallaci a shiyar kudu maso yammacin kasar Afrika ta Kudu, inda suka kashe mutane biyu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Wasu mahara sun kai farmaki cikin wani Masallaci a garin Malmezebury da ke kusa da jihar Cape Town a shiyar kudu maso yammacin kasar Afrika ta Kudu, inda suka soke mutane biyu da wuka har lahira tare da jikkata wasu adadi masu yawa.

Jami'an 'yan sandan Afrika ta Kudu sun samu nasarar hanzarta kawo dauki Masallacin, inda suka harbe maharan biyu har lahira. Rundunar 'yan sandan jihar Cape Town ta fara gudanar da bincike domin gano dalilin maharan na kai hari cikin Masallacin. 

 

3722811

 

 

 

 

 

 

 

captcha