IQNA

Jagora: Za A Kawar Da Isra’ila Da Himmar Al’ummomin Musulmi Na Duniya

23:54 - June 15, 2018
Lambar Labari: 3482760
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar: Matsalar haramtacciyar kasar Isra'ila ita ce rashin halalci, don haka da yardar Allah da kuma himmar al'ummar Musulmi, ko shakka babu za a kawar da ita da kuma kawo karshenta.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a yau din nan Juma'a a wata ganawa da yayi da manyan jami'an kasar Iran da kuma jakadun kasashen musulmi da suke Tehran bugu da kari kan dubun dubatan al'ummar Iran da suka kai masa ziyarar barka da salla inda ya ce daya daga cikin mafiya muhimmancin daukakar da al'ummar musulmi suke da ita shi ne hadin kan da suke da shi.

Ayatullah Khamenei ya ce babbar siyasar ma'abota girman kan duniya ita ce kokarin wajen haifar da rarrabuwan kai  tsakanin musulmi, don haka sai ya ce: hanya guda kawai ta fada da wannan siyasa ta Amurka da sahyoniyawa ita ce fahimtar makircinsu da kuma tsayin daka wajen fada da hakan.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa daya daga cikin manufofin samar da haramtacciyar kasar Isra'ila ita ce haifar da sabani da rikici tsakanin musulunci, to sai dai ya ce dukkanin alamu suna nuni da cewa ba za ta taba dawwama ba, don haka sai ya kirayi shugabanni da masana da masu fadi a ji na duniyar musulmi da su ba da himma da kuma sauke nauyin da ke wuyansu a wannan bangaren.

3708800

 

 

 

 

captcha