IQNA

An Karrama Mahardata Kur’ani Da Suka Nuna Kwazo A Gasar Kur’ani A Masar

23:26 - June 16, 2018
Lambar Labari: 3482763
Bangaren kasa da kasa, an karama mahardata kur’ani 350 da suka nuna kwazo a gasar kur’ani ta watan Ramadan a lardin Manufiyyah na kasar Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yaum sabi cewa, an karama mahardata kur’ani da suka nuna kwazo a gasar kur’ani ta watan Ramadan a lardin Manufiyyah na kasar Masar a garin Shatanuf.

Bayanin ya ce taron girmama mahardatan ya samu haartar jami’ai daga hukumar lardin na Manufiyyah, kamar yadda kuma malamai da masana daga sassa na lardin da wasu yankuna na kasar ta Masar sun halarci wurin.

Bisa ga al’ada ana gudanar da wannan gasar ne a kowace shekara a dukkanin bangarori na hardar kur’ani, kama daga hardar dukkanin kur’ani da kuam wani bangarensa.

Dukkanin wadanda suka halarci gasar dai matasa ne ‘yan makarantun firamare da sakandare.

3722956

 

 

 

 

 

 

captcha