IQNA

Gangamin Neman Hakkin dawo Da Wadanda Aka Kora A Palastine

22:48 - December 14, 2018
Lambar Labari: 3483215
Bangaren kasa da kasa, dubban Falastinawa sun gudanar da gangami domin jaddada hakkin komawar wadanda yahudawa suka kora daga kasarsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau kamar kowace Juma'a kuma kamar yadda aka saba, dubban Falastinawa sun gudanar da gangami a cikin yankunan Zirin gaza a kan iyaka da yankunasu da Isra'ila ta mamaye, domin jaddada hakkin komawar Falastinawa  wadanda yahudawa suka kora daga kasarsu tun fiye da shekaru arba'in da suka gabata.

Gangamin ya gudana tare da halartar dubban falastinawa daga bangarori daban-daban na kungiyoyin gwagwarmaya, wadanda suka jadadda cewa babu gudu abbu ja da baya wajen neman hakkokinsu da yahudawa suka kwace musu.

Tun daga lokacin fara wannan gangami a  ranar 30 ga wata maris da ya gabata, ya zuwa Falastinawa 248 ne suka yi shahada, dubu 26 kuma suka samu raunuka.

3772267

 

captcha