Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Aryana News ya bayar da rahoton cewa, a wani hari da sojojin Amurka suka kaddamar sun kashe babban kwamandan kungiyar daesh a kasar Afghansitan.
Janar Martin babban kwamandan rundunar sojin Amurka a kasar Afghanistan ya ce sun samu nasarar kashe babban kwamandan kungiyar Daesh a kasar Abu said Aurkazy bayan hartin da suka kai masa a yankin Nangahar.
Shi ma a nasa bangaren gwamnan yankin Nangagar ya bayyana cewa, wannan babbar nasara ce a kan kungiyar ta Daesh.