IQNA

Wani Alkali A Canada Ya Goyi bayan Hana Mata Saka Lullubi

10:33 - July 21, 2019
Lambar Labari: 3483862
Bangaren kasa da kasa, wani alkali jihar Cuebec a kasar Canada ya nuna goyon bayansa ga dokar da ta hana mata saka lullubia jihar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, Michael Yarco alkalin wata kotu  a jihar Cuebec da ke kasar Canada ya yi watsi da janye dokar hana mata saka lullubi.

Wannan hukunci na zuwa ne bayan da kungiyoyin musulmi da kuma wasu kungiyoyi masu kare hakkokin ‘yan adam suka suka shigar da kara kan dokar da aka kafa a majalisar dokokin jihar Cuebec mai lamba 21.

Wannan doka ta haramta wa mata yin amfani da lullubi a lokacin tuki ko a makarantu, ko masu aikin ‘yan sanda da kuma masu aiki jinya a  asibitoci.

Justin Trudeau firayi ministan kasar ta Canada, bayan kafa wannan doka, ya nuna rashin amincewarsa da dokar, inda yake ganin bai kamata a kayyade mata irin tufafin da za su saka ba, hakan yana a matsayin tauye hakkokinsu ne na zamantakewa.

3828379

 

captcha