IQNA

Erdogan Ya Zargi Amurka Da Kin Cika Masa Alkawali Dangane Da Kurdawan Arewacin Syria

23:52 - November 08, 2019
Lambar Labari: 3484236
Erdogan ya zargi gwamnatin Amurka da kin cika masa alkawali dangane da fitar da kurdawa masu dauke da makamai daga arewacin Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan, ya bayyana cewa gwamnatin Amurka taki cika masa alkawalin da ta dauka masa, dangane da fitar da kurdawa masu dauke da makamai daga arewacin Syria wadanda ya kira da ‘yan ta’adda.

Erdogan ya ce tun kafin wannan lokacin Amurka ta yi masa alkawalin cewa za ta fitar da Kurdawa na kungiyar YPG da suke dauke da makamai daga yankunan da ke kan iyakokin Syria da kuma Turkiya, saboda kasantuwarsu a wurin yana a matsayin barazana ta tsaro ga kasar Turkiya.

Ya ce Amurka bat a cika wannan alkawali ba, kuma a ganawar da zai da shugaban Amurka a cikin mai zuwa, zai bijiro da wannan Magana ga Donald Trump.

Amurka ta shelanta janyewa daga arewacin Syria a kwanakin baya domin baiwa Turkiya dammar shiga kasar ta Syria, amma daga bisani sojojin na Amurka sun koma bangarorin da rijoyoyin man kasar Syria suke domin ci gaba da kwasar garabasa.

 

 

3855325

 

 

 

captcha