IQNA

Sayyid Hassan Nasrullah Zai Gabatar Da Wani Jawabi

16:34 - August 07, 2020
Lambar Labari: 3485063
Tehran (IQNA) Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanonzai gabatar da wani jawabi dangane da halin da ake ciki a kasar da yankin.

Shafin alahad ya bayar da rahoton cewa, da yammacin yau Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da jawabi a yau wanda zai fara daga misalin karfe 17:30 na yamma agogon birnin Beirut.

A cikin jawabin nasa ana sa ran Sayyid Nasrullah zai tabo muhimman lamurra ne dangane da abin da ya shafi hatsarin da auku a birnin Beirut, da kuma matsayar Hizbullah kan hakan, da ma sauran lamurra da suka shafi yankin gabas ta tsakiya.

3915152

 

captcha