Shafin yada labarai na naba ya bayar da rahoton cewa, a yau, wasu daga cikin mabiya tafarkin ahlul bait sun gudanar da kwarya-kwaryan taro a cikin hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf domin tunawa da zagayowar lokacin Ghadir.
A bisa ga al’ada dai a irin wanann lokaci miliyoyin jama’a ne suke taruwa domin rawa wanann rana ta hanyar gudanar da taruka, da kuma yin jawabai kan matsayin wanna rana a cikin addinin muslucni.
A shekarar bana sakamkon matsalar cutar corona wannan yasa dole aka takaita tarukan sabanin yadda aka saba yia kowace shekara.
Kafin wanann lokacin cibiyar ad ke kula da hubbaren ta sanar da cewa ba za a gudanar da duk wani taro ba saboda tsoron bullar cutar corona, amma duk da haka an bar wasu mutane kadan domin gudanar da wannan taro.