Shafin jaridar al-Ahram ya bayar da rahoton cewa, shugaban kungiyar masu fasahar rubutu na kasar Masar Mas’ad Khudair ya bayyana cewa, an bayar da izinin rubuta cikakken kwafin kur’ani da kyakkyawan rubutu ga Abdulkarim Muhammad Marjan.
Marjan ya bayyana cewa, daya daga cikin manyan burukansa shi ne ya samu damar rubuta cikakken kur'ani da rubutu mai kyau wanda za a buga kuma jama'a su amfana da shi.
Ya ce Abdulkarim matashi ne mai himma matuka wanda ya cancanci hakan da jimawa, wanda a halin yanzu dalibi ne a jami’ar junubul wadi, inda yake karantar harshe da adabin larabci.