IQNA

Dubban Mabiya Addinai A Canada Sun Gudanar Da Jerin Gwano Domin Nuna Goyon Baya Ga Musulmi

22:56 - June 12, 2021
Lambar Labari: 3486004
Tehran (IQNA) Dubban mabiya addinai a Canada sun gudanar jerin gwano da gangami domin nuna goyon bayansu ga musulmin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, dubban mutane mabiya addinai daban-daban ne suka gudanar jerin gwano da gangami a binin London na jihar Ontario ta kasar Canada, domin nuna takaici kan abin da ya faru na kisan musulmi a birnin.

Dubban masu jerin gwanon sun yi gangami a daidai wurin da aka kashe musulmi hudu dukkaninsu iyalan gida guda, inda suka yi ta rera taken yin tir da Allawadai da nuna wa musulmi kyama ko kin jini a kasar da wasu suke yi a kasar.

Baya ga birnin London na jihar Ontario, an gudanar da irin wannan gangami a jihohi daban-daban na kasar Canada, da hakan ya hada har da biranan Ottawa da kuam Toronto, inda gangamin ya hada mabiya addinai daban-daban, da suka hada da kiristoci da yahudawa da mabiya wasu addinan na daban, kuam dukkaninsu suna nuna adawa da kin jinin musulmi.

A nasa bangaren Firayi ministan kasar Pakistan Imran Khan, ya gudanar da wata tattaunawa ta wayar tarho tare da firayi inistan kasar Canada Justin Redeau kan wannan lamarin, inda ya bukaci gwamnatin Canada da ta rufe duk wasu shafuka wadanda suke tunzura wadanda musulmi ba kan kin jinin musulmi da nuna musu kyama.

Firayi ministan kasar ta Canada dai ya nuna matukar kaduwarsa kan faruwar wannan lamari, inda ya sha alwashin cewa zai shiga kafar wando daya da masu nuna wa musulmi kin jini a kasar Canada.

3976938

 

captcha