IQNA

Kaddamar da gidan kayan tarihi a majalissar kur'ani ta Sharjah

14:45 - July 05, 2022
Lambar Labari: 3487507
Tehran (IQNA) Majalisar kur'ani mai tsarki ta Sharjah ta kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta kaddamar da wani gidan adana kayan tarihi a wannan wuri domin nuna sabbin kyaututtukan da Sarkin Sharjah ya yi masa, da suka hada da tarin kur'ani da ba kasafai ba.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na WAM cewa, wannan majalissar ta ware wani gidan tarihi domin nuna sabbin kyaututtuka na “Sultan bin Muhammad Al-Qasim” dan majalisar koli ta Sharjah kuma mai mulki kuma sarkin wannan birni.

A kwanakin baya ne mai martaba sarkin Sharjah ya bayar da gudunmuwar tarin kur’ani mai tsarki na tarihi ga wannan jama’a, wanda za a baje kolin a wannan gidan kayan gargajiya, kuma za a baje kolin ga masoya da maziyartan taron.

Babban sakataren majalisar kur'ani mai tsarki ta Sharjah Shirzad Abdul Rahman Taher ya bayyana cewa: A yayin kaddamar da wannan gidan kayan gargajiya, maziyartan za su samu damar ganin sabbin kayayyakin da sarkin Sharjah ya bayar a dakin adana kayan tarihi na kur'ani mai tsarki na musamman.

Ya kara da cewa: Majalisar kur'ani mai tsarki ta Sharjah a halin yanzu tana kunshe da tarin kur'ani mai tsarki na tarihi da kur'ani da aka rubuta a fata da sauran ayyukan kur'ani da ba kasafai ake yin su ba, wadanda wasu daga cikinsu shekaru 1300 ne da suka shafe shekaru daban-daban tun daga Hijira na biyu zuwa yau.

Har ila yau Shirzad Abdul Rahman Tahir ya ce: An tattara wadannan kur'ani ne daga yankuna da garuruwa daban-daban na Musulunci, kuma galibinsu kyauta ne daga sarkin Sharjah, wanda daya ne daga cikin masu goyon bayan majalisar kur'ani mai tsarki ta Sharjah.

4068645

 

captcha