IQNA

An Yi Allawadai Da Amincewa Da Quds A Matsayin Birnin Isra’ila Da Chek Ta Yi

23:57 - December 25, 2018
Lambar Labari: 3483252
Bangaren kasa da kasa, majalisar kungiyar kasashen larabawa ta yi Allawadai da kakkausar murya kan amincewar da Chek ta yi da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, a zaman da majalisar kungiyar kasashen larabawa ta yi a jiya, ta Allawadai da kakkausar murya kan amincewar da Chek ta yi da birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra’ila, tare da bayyana hakan a matsa keta dokoki na kasa da kasa.

Mash’al Bin faham al-silmi mataimakin shugaban majalisar kungiyar kasashen larabawa ya bayyana cewa, a shekara ta 1988 kasar Chek ta amince da Falastinu a matsayin kasa mai cin gishin kanta, amma matakin da gwamnati mai ci a yanzu a kasar ta dauka, ya sabawa matsayar da aka san al’ummar kasar a kanta dangane da Palastine.

A ranar 21 ga watan Disamban 2017 majalisar dinkin duniya ta yi fitar da kudiri da ke yin watsi da matakin Donald Trump ya dauka, na shelanta Quds a matsayin abban birnin Isra’ila.

Kasar Chek ta ce tana shirin dauke ofishin jakadancinta daga Tel aviv zuwa Quds na ba da jimawa ba.

3775454

 

captcha