IQNA

Iran Ta Kirayi Taliban Da Ta Kare Lafiyar Jami'an Diflomasiyya Na Kasashen Ketare Da Ke Harat

21:22 - August 14, 2021
Lambar Labari: 3486201
Tehran (IQNA) Iran ta bukaci kungiyar Taliban da ta tabbatar da bayar da kariya ga wuraren diflomasiyya da suke cikin birnin Harat.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bukaci kungiyar Taliban da ta tabbatar da bayar da kariya ga wuraren diflomasiyya da suke cikin birnin Harat da ta kwace iko da shi jiya a kasar Afghanistan.

A cikin wani jawabi da ya fitar a jiya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ya bayyana cewa, hakika Iran ta damu matuka dangane da irin yanayin da kasar Afghanistan ta samu kanta a ciki.

Ya ce birnin Harat wanda shi ne birni na biyu mafi muhimmanci a kasar Afghanistan wanda kuma a halin yanzu ya fada karkashin ikon kungiyar Taliban, ya zama wajibi a kan kungiyar da ta bayar da kariya ga ofisoshin diflomasiyya na kasashen ketare da suke a birnin, da kuma kare rayukan fararen hula, da kuma bayar da kariya ga jami’an diflomasiyya na kasashen waje.

A nata bangaren rundunar sojin kasar Iran ta sanar da cewa, babu wata barazana a kan iyakokin kasar da kuma kasar Afghanistan, komai yana tafiya ba tare da wata matsala ba.

Gwamnatin kasar Iran ta kara jaddada kiranta ga dukkanin bangarori a kasar ta Afghanistan, da hakan ya hada da gwamnatin kasar da kuma kungiyar Taliban, da su rungumi hanyar tattaunawa da kuma warware matsalolin kasar ta hanyar yin sulhu da kuma fahimtar juna.

3990355

 

 

 

 

captcha