IQNA

An Gudanar Da Gasar Hardar Kur’anI Mai Tsarki A Rwanda

23:14 - October 01, 2014
Lambar Labari: 1456412
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarkia kasar Rwanda tare da halartar mahardata da suka kara da juna a wannan gasa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo cewa, an gudanar da wannan gasar ne tare da halartar mahardata 50 wadanda dukakninsu musulmi na kasar, kuma an guadanmr da gasar ne a matakai daban-daban, da hakan ya hada da matai na hardar kur’ani baki daya, sai kuma mataki na biyu hardar rabi, da kuma na hardar kwata.
Bayan kammaa gasa a zaman karshe an bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo a wannan gasa, dukkanin mahalartan dais un nuna gamsuwarsu matuka dangane da yadda ta gudana da kuma yadda aka yi tsari mai matukar kayatarwa ga kowa.
An gudanar da bayanai da kuma laccoci a lokacin bude gasar da kuma lokacin rufe ta, daga cikin abin da aka mayar da hankali kansa har da tunatar da matasa musulmi da kuma kokarin jan hankulansu zuwa lamarin kur’ani mai tsarki, wanda a cikinsa shiryar dukaknin talikai take ciki.
1455634

Abubuwan Da Ya Shafa: Rwanda
captcha