IQNA

Daesh Ta Dauki Nauyin Harin Birnin Istanbul

21:48 - January 02, 2017
Lambar Labari: 3481095
Bangaren kasa da kasa, kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh ta dauki nauyin kaddamar da harin birnin Istanbul a wurin shkatawa na Rina da ke birnin.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Sabah ta kasar Turkiya cewa, kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh ta dauki nauyin kaddamar da hari a wurin shkatawa na Rina da ke birnin Istanbul.

Wasu majiyoyi a kasar ta Turkiya sun nakalto daga shafin kammafanin dillancin labarai na reauters cewa, harin wanda aka kai a daren sabuwar shekarar miladiyya a wurin shakatawar da ke birnin Istanbul, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 39, yayin da wasu 69 kuam suka samu raunuka.

Abin tuni a na koa jiya ma wani dan bindigar ya sake kaddamar da wani hari da bindiga a kan masallacin Pasha da ke cikin birnin na Istanbul, inda ya jikka wasu mutane biyu a kalla.

Kasar Turkiya dai ta kasance a sahun gaba wajen daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'addan Daesh, wadanda a halin yanzu suka dawo a kanta.

3558871


captcha