IQNA

Malmin Kirista A Masar Ya Ce Addinin Muslunci Ya Barranta Daga Daesh

17:47 - July 14, 2017
Lambar Labari: 3481700
Bangaren kasa da kasa, Jagoran kiristoci mabiya darikar katolika a kasar Masar ya bayyana addinin muslunci da cewa addini ne da ba shi da alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Daesh da makamantansu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, Yuhana Qalta Jagoran kiristoci mabiya darikar katolika a kasar Masar,a yayin gabatar da wani jawabi a jiya a babban dakin karatu na tarihi da ke birnin iskandariya a kasar masar ya bayyana cewa, babu wani addini da aka saukar daga sama da ke yin kira zuwa ga tashin hankali ko kashe dan adam ba gaira ba sabar.

Ya ce dukkanin addinai da suka zo daga Allah suna yin kira ne zuwa ga imani da bautar Allah da kuma koyar da dan adama kyawawan halaye da tausayi da jin kan da yada amici a doron kasa, a kan duk wani mutum da ke danganta kansa da wani addini da aka saukar daga sama kuma yake aikata sabanin hakan, to addininsa ya barranta daga ikinsa, a kan masu danganta ayyukan ta'addanci irin na ISIS da makamantansu ga addinin muslunci suna yin kure.

Yuhana Qalta ya ce dakin karatu na Iskandariyya an bude shi ne tun shekaru 300 kafin haihuwar annabi Isa (AS) kuma ya kama ya i gaba da zama wuri na hada mabiya addinai da wayar da kansu a kan manufar sakon addinai da Allah ya saukar daga sama.

3618647


captcha