IQNA

Baje Kolin Sunayen Allah Kyawawa Da Harsuna 10 A Gefen Masallacin Annabi

17:16 - September 05, 2017
Lambar Labari: 3481867
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani baj ekolin sunayen Allah kyawawa a gefen masallacin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa a Madina.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya abyar da rahoton cewa, a jiya fara gudanar da wani baj ekolin sunayen Allah kyawawa a gefen masalalcin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa a birnin Madinah mai alfarma.

Raja bin Aish Aljahani shi ne shugaban wannan baje koli ya bayyana cewa, wannan yana daga cikin ayyukan da aka fara yi baya-bayan nan da nufin kara fio da irin fasahohi na musulunci.

Ya ce tun da aka fara gudanar da wannan baje koli kusan shekaru uku zuwa hudu da suka gabata, ya zuwa ya samu karbuwa daga masu ziyara a wannan wuri mai tsarki daga kasashen duniya.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, ganin cewa wannan yana daga cikin wurare da ke samun masu ziyara daga kasashen duniya, wannan ya sanya an tarjama wadannan sunaye na Allah masu tsarkia cikin harsuna goma na duniya.

An fara wannan baje koli ne tun a cikin shekara ta 1435 bayan hijirar manzon Allah, kuma ana ci gaba da gudanar da shia kowace shekara.

Dan rahoton tashar alalam da ya aiko wa tashar rahotanni aikin hajjin bana ya ziyarci wurin ya kuma shirya rahoto.

3638684


captcha