IQNA

An Fara Gudanar Da Zaman Taron Musulmin Arewacin Amurka A Toronto

23:46 - December 22, 2017
Lambar Labari: 3482226
Bangaren kasa da kasa, musulmin arewacin Amurka sun fara gudana da zaman babban taronsu karo na goma sha shida a birin Toronto na kasar Canada.

 

Kamfanin dillanci labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Risconvention cewa, a yau musulmin arewacin Amurka sun fara gudana da zaman babban taronsu karo na goma sha shida a birin Toronto na kasar Canada domin tattauna muhimman lamurra da suka shafe su.

Taron wanda aka fara gudanawa a yau, yana saun halartar malamai da masana musulmi daga sassa na arewacin Amurka, da hakan ya hada da kasar ta Canada da kuma jahohin Amurka.

Babbar manufar gudanar da wannan taro da ake yi a kowace na musulmin arewacin Amurka, ita wayar da kan muuslmi dangane da hakianin muslunci da koyarwarsa, da kuma yadda ya kamata musulmi ya kasance, musamman a cikin kasashe na yammacin turai.

Kimanin mutanr dubu 20 ne da suke halartar wannan taro daga sassa daban-daban na arewacin Amurka, kuma taron zai dauki tsawon kwanki uku ana gudana da shi.

Daga cikin abubuwan da taron yake mayar da hankali a kans a wanan karo, har da batun danganta musunci da ta’addanci da ake yi  wannan zaman, da kuma karuwar kyamar musulmi a cikin yankunan arewacin Amurka.

A halin yanzu dai musulmi su ne kashi 3 cikin dari na al’ummar kasar Canada, inda alkalumma suka nuna cewa musulunci karu da kashi 82  akasar a cikin ‘yan shekarun bayan nan.

3674996

 

captcha