IQNA

Sayyid Nasrullah: Saudiyya Ta Yi Wa Syria Tayin Katse Alaka Da Iran Da Hizbullah

23:40 - March 27, 2018
Lambar Labari: 3482514
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah sayyid Hassan nasrullah ya bayyana cewa an gudanar da wani zama tsakanin manyan jami'an gwamnatin Saudiyya da Syria inda Saudiyya ta bukaci Syria da ta yanke alaka da Iran da Hizbullah.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Sayyid hasan Nasrullah ya bayyana hakan nea  wata zantawa da ta hada shi da jaridar Alakhabr ta kasar Lebanon, wadda aka buga a yau Talata.

A cikin zantawar, Sayyid nasrullah ya bayyana cewa; Saudiyya ta bukaci Syria da yanke alakarta ta baki daya ne da Iran da kuma kungiyar Hizbullah, idan ta yi haka ita kuma za ta daina taimaka ma 'yan ta'adda da suke kai hare-hare a  cikin kasar ta Syria.

Bababn sakataren kungiyar Hizbullah yace ko shakka babu wannan wani shiri ne da ke nufin kassara irin gudunmawar da kungiyar Hizbullah ta bayar wajen karya lagon 'yan ta'adda, da kuma hana Amurka da Isr'ila da 'yan korensu cimma burinsu a cikin kasshen Syria da Iraki.

Baya ga haka kuma ya cea  halin yanzu ana yin amfani da dukkanin hanyoyi domin kawo ma kungiyar Hizbullah cikas a ciki da wajen Lebanon, wanda kuma a cewarsa da yardar Allahyardarm ba zai yi nasara ba.

Ya ce a halin yanzu kungiyar Hizbullah tana da karfin da bata taba mallakar irinsa ba a tarihinta, kuma a shirye take ta ci gaba da aiwatar da dukkanin ayyukanta domin murkushe 'yan ta'adda masu yi Amurka aiki domin rusa kasashen larabawa da na musulmi.

Dangane da zaben Lebanon kuma, ya bayyan acewa Amurka da 'yan korenta sun dage a kan sai sun mayar da Hizbullah saniyar ware a cikin ahrkokin siyasar Lebanon, ya ce wannan mafarki shi ma ba zai tabbata ba kamar irinsa da dama da suka yi a baya, ba su tabbata ba.

3702145

 

 

captcha