IQNA

Hukumar WHO Ta Goyi Bayan Saudiyya Kan Takaita Yawan Maniyyata A Bana

23:15 - June 25, 2020
Lambar Labari: 3484928
Tehran (IQNA) babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO ya bayyana matakin da Saudiyya ta dauka na takaiya yawan masu aikin hajjin bana da cewa mataki ne mai kyau.

Tashar CNN ta bayar da rahoton cewa, Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanon ya bayyana cewa, matakin da Saudiyya ta dauka yana da matukar muhimmanci wajen kare rayukan jama’a da kuma dakile yaduwar cutar a cikin kasar da ma kasashen duniya.

Ya ce kafin daukar wannan mataki, saudiyya ta yi shawara da hukumar lafiya ta duniya, kuma sun amince da hakan, domin kuwa mataki da zai taimaka matuka.

Tedros ya ce wannan yana daya daga cikin matakai mafi wahala da aka dauka tun bayan bullar cutar corona, domin aikin hajji aiki ne na ibada, wanda miliyoyin musulmi sun yi niyyar sauke farali a bana, wanda kuma tabbas daukar wannan mataki ba zai yi musu dadi, kamar yadda bai yi wa hukumar lafiya da ma gwamnatin ta Saudiyya dadi ba, amma kuam daukarsa shi ne yafi dacewa saboda larurara da kuma halin da ake ciki.

Gwamnatin kasar Saudiyya dai ta sanar a hukumance kan cewa, a wannan shekarar da muke ciki, ‘yan kasar ne gami da ‘yan kasashen ketare da suke zaune cikin kasar kawai za su yi aikin hajjin ba, kuma su ma za  akayyade adadinsu ta yadda ba zai yi yawan da zai jawo cunkoso ba.

 

3906870

 

captcha