IQNA

An Dakatar Da Bude Wasu Wuraren Ibada A Wata Jiha Ta Najeriya

19:47 - July 18, 2020
Lambar Labari: 3484996
Tehran (IQNA) an dakatar da bude wuraren ibada a wata daya daga cikin jihohin Najeriya.

Jaridar Vanguard ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin jihar Ekiti ta bayyana cewa, bisa la'akari da matsaloli da ake fuskanta ta fuskacin kiwon lafiya, wannan yasa aka dakatar da bude wuraren ibada a wata daya daga cikin jihohin Najeriya.

Kwamishinan lafiya na jihar Ekiti ya bayyana cewa, za a ci gaba da rufe wasu masalatai da coci-coci saboda malamansu sn bayyana cewa ba za su iya kiyaye dukkanin sharuddan da aka gindaya musu ba.

Ya kara da cewa yara da yan kasa da shekaru 12 da kuma dattijai sama da shekaru 65, an hana su zuwa masallatai da wuraren ibada.

Yanz haka dai kimanin mutane 772 cutar corona ta lakume rayukansu a Najeriya.

 

 

3911083

 

 

 

captcha