IQNA

Daftarin Kudirin Amurka Kan Iran Ya Fadi Kasa Warwas A Kwamitin Tsaro

23:08 - August 15, 2020
Lambar Labari: 3485086
Tehran (IQNA) Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya yi watsi da sabon daftrain kudirin Amurka da ke neman a sabunta takunkumin hana Iran saye da sayar da makamai.

A zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar jiya domin kada kuri’a kan sabon daftarin kudirin Amurka, da ke neman a sabunta takunkumin hana Iran saye da sayar da makamai, kwamitin ya yi watsi da daftarin kudirin na Amurka.

Kasashen China da Rasha sun yi fatali da wannan daftarin kudiri ta hanyar hawa kujerar naki, yayin da kasashen Burtaniya, Jamus da Faransa da wasu kasashe 8 mambobin kwamitin suka ki kada kuri’a, inda tsakanin kasashe mambobin kwamitin su 15, Amurka da jamhuriyar Dominican kawai suka kada kuri’ar amincewa da daftrain kudirin na Amurka a kan Iran.

A nasa bangaren jakadan Iran a majalisar dinkin duniya Majid Takht Ravanchi, jim kadan bayan kammala zaman ya bayyana cewa, Amurka ta yi hankoron mayar da Iran saniyar ware a zaman kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, amma kuma sai kasashen duniya suka mayar da ita Amurka ta zama ita ce saniyar waren.

Ya ce kafin wannan lokacin Amurka ta yi ta babatun cewa, hawa kujerar naki da kasashen Rasha da China za su yi kawai zai iya hana daftarin kudirin nata wucewa, amma kuma a zaman na jiya ko da babu hawa kujerar naki daga Rasha da China, to daftarin kudirin ba zai wuce ba, domin dukkanin mambobin kwamitin tsaron sun yi watsi da shi, in banda ita kanta Amurka da wata kasa guda daya.

 

 

 

3916623

 

captcha