IQNA

Ayatollah Sistani ya Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Sarkin Kuwait

22:58 - October 03, 2020
Lambar Labari: 3485240
Tehran (IQNA) babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sistani ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar sarkin kasar Kuwait.

Kamfanin dillanicn labaran nina ya bayar da rahoto daga kasar Iraki cewa,a  yau babban malamin babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar sarkin kasar Kuwait.

Babban malamin ya bayyana rasuwar sarkin Kuwait Sabah Ahmad Al-jabir Al-sabah da cewa babban rashi ne da aka yi, kasantuwar cewa shi mutum ne da ya kasance yana damuwa da lamarin al’umma a matsayi na kasarsa da ma duniyar musulmi baki daya.

Bayanin Ayatollah Sistani ya kara da cewa, marigayin ya yi amfani da hikima da hangen nesa wajen daukar matakai da dama wadanda suke maslaha ga al’umma, saboda haka rashinsa babban rashi ne dab a za a manta da shi ba.

Daga karshe ya roki Allah da ya yi masa rahma da gafara, kuma baiwa iyalansa hakurin rashinsa, kuma ya kara albarka da ci gaba ga kasar Kuwait da ma sauran dukkanin kasashen musulmi.

 

3926767

 

Abubuwan Da Ya Shafa: baiwa iyalansa hakurin rashinsa kasar Kuwait
captcha