IQNA

Majalisar Dokokin Amurka Ta Tabbatar Da Biden A Matsayin Zababben Shugaban Kasa

20:10 - January 07, 2021
Lambar Labari: 3485532
Tehran (IQNA) majalisar dokokin Amurka ta tabbatar da Joe Biden a matsayin zababben shugaban kasa.

Rahotanni daga kasar Amurka sun tabbatar da cewa, majalisar dokokin kasar ta tabbatar da Joe Biden a matsayin wanda ya lashe zaben shugaba kasar a hukumance, bayan da majalisar ta ci gaba da zamanta, biyo bayan farmakin da magoya bayan Trump suka kaddamar kan majalisar, inda suka hana majalisar gudanar da zama.

Farmakin magoya bayan Trump dai ya tilasta majalisar dakatar da zaman da take gudanarwa dangane da sakamakon zabe, inda Trump din ya rika zuga su da kuma tunzura su domin su kawo cikas ga zaman, wanda Trump ya yi imanin cewa za a tabbatar da Joe Biden a matsayin wanda ya lashen shugaban kasar da aka gudanar.

Daga bisani bayan da jami’an tsaro suka samu nasarar fitar da masu tarzomar, majalisar ta ci gaba da gudanar da zamanta, inda ta tabbatar da sahihancin zaben da aka yi wa Biden.

Kungiyar tarayyar turai ta yi Allawadai da abin da ya faru, tare da bayyana hakan a matsayin keta hurumin dimukradiyya, tare da kira ga bangarorin da suka sha kayi a zaben da amince da shan kayin da suka yi, maimkaon tayar da tarzoma.

3946285

 

 

 

captcha