IQNA

Mutane Dubu 500 Ne Suka Ziyarci Lambun Kur’ani A Birnin Dubai

22:39 - January 27, 2021
Lambar Labari: 3485593
Tehran (IQNA) lambun kur’ani da ke birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa ya zama daya cikin muhimman wurare da mutane suke ziyarta a birnin.

Shafin yada labarai na jaridar Alkhalij ya bayar da rahoton cewa, Dawud Almuhajiri babban darakta mai kula da lambun kur’ani a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa ya bayyana cewa, daga watan Afirilun 2019 da aka bude lambun kur’ani ya zuwa mutane sama da miliyan daya da dubu 500 ne suka ziyarci wurin.

Ya  ce a cikin shekara ta 2020 da ta gabata kuwa, akalla mutane dubu 500 ne suka ziyarci wannan wuri, domin gane wa idanunsu abubuwan da aka tanada a ciki.

Ya ce wannan ba na bude ido ne kawai ba, domin kuwa wuri da masu bincike kan ilmomin kur’ani suke amfanuwa da shi matuka, wanda yake taimaka musu wajen samun wasu bayanai da suke bukata cikin sauki.

An dai gina wannan wuri ne mai fadi mita murabba’i 600, wanda ya kunshi abubuwa daban-daban, baya ga wurare da aka kebance domin ajiye wasu abubuwa na tarihi, an kuma kebance wurin ajiyar abubuwa daban-daban da aka ambata a cikin kur’ani mai tsarki

Baya ga haka kuma akwai wurin salla da kuma dakin karatu, wanda aka saka littafai daban-daban musamma wadanda suka danganci ilmomin kur’ani mai tsarki, da kuma hadisan ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.

Wurin yana samun ziyarar mutane musulmi da ma wadanda ba musulmi, wadanda suke son sanin wani abu dangane da kur’ani mai tsarki.

3950207

 

 

captcha