IQNA

Kuwait Ta Kafa Dokar Hana Shigo Da Kur’anai A Kasar Ba Tare Da Izini Ba

17:23 - June 27, 2021
Lambar Labari: 3486053
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Kuwait ta kafa dokar hana shigo da kwafin kur’anai a cikin kasar ba tare da izini ba.

Shafin jaridar Alwatan ta kasar Kuwait ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar ta kafa dokar hana shigo da kwafin kur’anai a cikin kasar ba tare da izini ba, da hakan ya hada har da buga kwafin kur’anai ko liffan hadisan ma’aiki (SAW) a cikin kasar.

Rahoton ya ce mahukuntan kasar ta Kuwait sun sanar da cewa sun dauki wannan matakin ne sakamakon matsalolin da ake samu wajen buga littafai, wanda hakan ya kan shafi har da kwafin kur’ani da kuma lifafan hadisan ma’aiki, wanda hakan kuma yana da babban hadari.

A kan haka bayanin ya ce, duk wanda zai shigo da wani adadi na kwafin kur’ani a  cikin kasar, dole a tantance da kuma tabbatar da cewa an buga su ba tare da wani kure ba, tare da samun takardun izini a hukumance.

Haka nan kuma masu buga kur’ani a cikin gida dole ne kafin su fara sayarwa ko kuma fitar das u zuwa kasashen ketare, dole ne sai an tabbatar da ingancin bugun da kuma tabbatar da cewa babu kure a cikin tsarin surori ko ayoyin kur’ani baki daya kafin fitar da su, wanda kuma ya saba hakan, to zai fusaknci tara mai tsanani.

3980274

 

 

captcha