IQNA

Matashi Dan Kasar Masar Da Ya Hardace Kur'ani Da Kira'oi Goma

20:39 - August 31, 2021
Lambar Labari: 3486257
Tehran (IQNA) Muhammad Tajuddin Kamal matashi ne dan kasar Masar da ya hardace kur'ani da kira'oi goma.

Shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Tajuddin Kamal matashi ne dan kasar Masar da wanda ya samu nasarar hardace kur'ani da kira'oi goma.

matashin dai an haife shi ne a kauyen Al'adu da ke cike cikin gundumar alminya a kasar Masar, sannan kuma ya samu tarbiya ta kur'ani tun daga wajen mahaifansa.

Ya ce dukkanin 'yan gidansu sun hardace kur'ani baki daya, sannan kuma mahaifansa ne suka fara koyar da shi karatu da hardar kur'ani mai tsarki.

Bayan wani lokaci kuma ya shiga makaranta, amma duk da haka bai tsaya da hardar kur'ani ya ci gaba har ya kammala, daga lokacin kuma ya fara koyon karatu da kira'oi daban-daban.

Yanzu haka dai wannan matashi yana daga cikin makaranta mafi shahara a bangaren karatu da hardar kur'ani mai tsarki a cikin lardin Alminya da ke kasar masar.

 

3993405

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gunduma kasar masar jarida matashi
captcha