A cewar Al-Madina, masu kula da Masallacin Harami bisa al'adar kowace shekara da jajibirin lokacin Hajji na shekarar 1443, bayan an yi sallar Magriba a daren jiya, sai suka daga labulen dakin Ka'aba da mita uku, sannan suka sanya farin kyalle mai fadin mita 2 a kusa da shi.
Babban Darakta na Al-Masjid Al-Haram ya sanar da cewa, 'yan sa'o'i kadan bayan Magriba a yammacin Lahadi an sanya wani farin kyalle na auduga a dukkan bangarori hudu na dakin Ka'aba yayin da mahajjata ke gudanar da ibada da dawafi a Dakin Allah.
Da wannan ibada, yayin da ake saka labulen dakin Ka’aba, an lullube shi da ihrami kuma an lullube shi da fararen kyallaye , ta haka ne ake shirya kwanakin aikin Hajji, wanda zai fara a kasa da kwana 20 masu zuwa.