IQNA

Masu Ziyara Fiye da miliyan 2 daga Iran suka isa Iraki a ƙafa

15:55 - September 11, 2022
Lambar Labari: 3487834
Tehran (IQNA) Hukumar kula da kan iyaka ta kasar Iraki ta sanar da cewa sama da maziyarta na Iran miliyan biyu ne suka shiga kasar ta hanyar tsallaka kasa domin gudanar da bukukuwan Arbaeen.

Masu Ziyara Fiye da miliyan 2 daga Iran suka isa Iraki a ƙafa

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bagadaza Al-Youm cewa, shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasar Iraki Omar Al-Waili ya sanar da cewa, an amince da tsarin shigar maziyarta  ta mashigar kan iyakoki bisa tsarin babban tsarin tsaro da ke karkashin kulawar hukumar kula da iyakokin kasar, a cewar ministan harkokin cikin gida.

Ana aiwatar da matakan da suka wajaba bisa tsarin da aka amince da su, wanda ya hada da duba dukkan masu ziyara idan sun iso, da kuma buga fasfo, kuma mahajjata suna shiga cikin kasar Iraki ne kawai da takardar shaidar da ofishin fasfo ya amince da ita.

A yayin da yake ishara da babban hadin kai tsakanin hukumomin kan iyaka da ma'aikatar harkokin cikin gida da rundunar hadin gwiwa da kuma larduna a kasar Iraki, Al-Waeli ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu sama da masu ziyara na Iran miliyan biyu ne suka shiga kasar Irakin ta mashigar kan iyakokin kasar.

Kasar Iran ta mika godiya ga mahukuntan kasar Iraki kan kulawar da suka bayar wajen tarbar maziyarta daga kasar ta Iran da ma kasashen duniya.

 

4084600

 

captcha