IQNA

Dan wasan kwallon kafa na Morocco: Alqur'ani shine abokina na farko kafin kowane dan wasa

15:34 - November 12, 2022
Lambar Labari: 3488161
Tehran (IQNA) Matashin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Morocco yayi magana kan alakar sa da kur'ani mai tsarki a cikin wani faifan bidiyo da shafukan sada zumunta suka yi maraba da shi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na “Site” faifan bidiyo na Bilal Al-Khunos Al-Tondous dan wasan kwallon kafa na kasar Moroko da ke bayyana ra’ayinsa kan kur’ani mai tsarki ya zama kan gaba a shafukan sada zumunta.

An kira Al-Khunos mai shekaru 18 da haihuwa da mamaki bayan ya fito cikin jerin 'yan wasan kasar Morocco na karshe da za su halarci gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a shekara ta 2022.

A wata hira da ya yi da wani shafin wasanni, Al-Khunos ya yi bayani a kan addininsa da kyawawan halaye inda ya ce ya dogara da littafin Allah sosai kuma kafin kowace gasa da kuma lokacin horo a hukumance abokin aikinsa na farko shi ne kur’ani mai tsarki.

Yana cewa: Ina alfahari da cewa addinina shi ne Musulunci. Na taso cikin iyali mai yawan addini kuma zan ci gaba da karatun Alqur'ani da addu'a har zuwa karshen rayuwata. Wannan yana taimaka mini da yawa.

Dan wasan na Morocco ya bayyana cewa: Karatun kur'ani yana ba ni kwanciyar hankali kuma yana taimaka min wajen cimma burina.

 

4098826

 

 

captcha