IQNA

Dalibai sama da dubu 4 sun amfana daga tarukan kur'ani a kasar Kuwait

16:40 - December 28, 2022
Lambar Labari: 3488413
Tehran (IQNA) Kungiyar agaji ta Najat a kasar Kuwait ta sanar da cewa sama da dalibai maza da mata ‘yan kasar Kuwait sama da dubu 4,600 ne suka yi amfani da ayyukan koyar da kur’ani na wannan al’umma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Kuwait cewa, an gudanar da wadannan ayyuka ne ta hanyar gudanar da harkokin kur’ani mai tsarki da Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam Jami’ar kasar Kuwait.

A zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kuwait Jazaa Al-Saileh, jami'in da ke kula da gudanar da wadannan tarukan ya ce: Ya kamata a yi la'akari da wannan muhimmiyar nasara da ta yi daidai da burin gwamnatin Kuwait na tallafawa shirye-shiryen hidima a cikin kasar, musamman ma. shirye-shiryen sadaka.

Al-Saileh ya kara da cewa: Mutane 3,650 ne suka ci gajiyar tarukan na yau da kullum, kuma kimanin mutane 950 ne suka amfana da tarukan marecen kur'ani, kuma daga cikinsu dalibai mata 84 ne suka samu nasarar kammala kur'ani.

Ya bayyana wadannan alkaluma a matsayin wata babbar nasara ta fuskar yawan tarurrukan da aka gudanar, da masu amfani da wadannan tarukan, da ire-iren tarukan kur’ani.

A cewarsa, hanyar koyar da kur’ani a cikin wadannan zaman ita ce, a fara jarraba wadanda za su yi takara sannan kuma gwargwadon iyawar kowane dan takara zai koyi kur’ani mai tsarki a zaman da ya dace da wadannan abubuwan.

Ana gudanar da wadannan tarurrukan ne bisa hanyoyin kimiyya da ilimi na zamani, kuma manufarsu ita ce karawa da karfafa ilimin kur'ani na dalibai.

 

 

4110268

 

 

captcha