IQNA

Adadin Falasdinawa Da suka Yi Shahada Ya Tasamma 3500

17:05 - October 18, 2023
Lambar Labari: 3489997
Gaza (IQNA) A cewar sanarwar da ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar, adadin shahidan Falasdinawa a lokacin cin zarafi na gwamnatin Sahayoniyya ya kai kimanin mutane 3,500, yayin da sama da mutane 12,000 suka jikkata.

A rahoton tashar al-Masira, kakakin ma'aikatar lafiya ta Falasdinu Ashraf al-Qdara ya sanar da shahadar Palasdinawa 3,478 tare da raunata wasu 12,065 sakamakon munanan hare-haren da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai a zirin Gaza.

Al-Qadara ya sanar da cewa: Shigar da makiya ke yi a matakin kai hari kan asibitoci da kuma nuna kyama ga kisan gillar da ba za a iya misaltawa ba a asibitin Al-Mu'amdani, ana daukarsa a matsayin barazana ga tsarin kiwon lafiya.

Ya ci gaba da cewa: Adadin wadanda aka kashe a wannan gagarumin kisan gilla da makiya suka yi a asibitin Al-Mu’amdani ya kai shahidai 471 da raunata 314. An kuma bayyana cewa yanayin mutane 28 da suka jikkata na da muni.

Ya jaddada cewa: Kashi 70% na wadanda hare-haren Isra'ila ya shafa a Gaza yara ne da mata da kuma tsofaffi. A cikin wadannan laifuffuka, an kai hari kan iyalai 433, kuma gawarwakin shahidan wadannan iyalai 2421 ne kawai aka samu, kuma daruruwansu har yanzu suna karkashin baraguzan ginin.

Al-Qadara ya kara da cewa: Ma'aikatar lafiya ta kasar ta samu sakonni 1,300 kan mutanen da suka makale a karkashin baraguzan ginin, wadanda 600 daga cikinsu yara ne. Muna sa ran cewa wasu daga cikin mutanen da suka rasa matsugunansu na raye, amma da wuya a kai su, saboda ci gaba da tashin bama-bamai da rashin kayan aiki.

Kakakin ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ya yi gargadin cewa bayan da asibitocin suka shiga wani mataki na rugujewa a aikace, sa'o'i masu zuwa za su yi matukar tasiri a tsarin samar da kiwon lafiya ga marasa lafiya da wadanda suka jikkata a nan gaba.

 

4176333

 

Abubuwan Da Ya Shafa: falastinawa shahada gaza kisan gilla asibitoci
captcha