IQNA

An samu karuwar laifukan kyama da ake yiwa musulmi a birnin Landan

15:44 - October 28, 2023
Lambar Labari: 3490052
Landan (IQNA) A cewar sanarwar da rundunar ‘yan sandan birnin Landan ta fitar bayan harin da guguwar ta Al-Aqsa ta kai, laifukan nuna kyama ga musulmi a birnin Landan sun ninka a cikin makon da ya gabata.

Shafin Al-Jarida ya bayar da rahoton cewa, alkaluman da 'yan sandan birnin Landan suka buga sun nuna cewa laifukan da suka shafi kyamar Musulunci sun karu bayan fara farmakin da guguwar Al-Aqsa ta yi kan gwamnatin sahyoniyawa.

Tun bayan da aka fara rikici a yankunan da aka mamaye a Burtaniya da ma wasu wurare ana zaman dar-dar, lamarin da ya janyo zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa. A wannan lokacin ne kuma kungiyoyin yahudawan suka gudanar da jerin gwano domin bayyana goyon bayansu ga Isra'ilawa.

A cewar Kyle Gordon, jami’in ‘yan sandan birnin Landan, an aikata laifukan kyamar Musulunci har 174 a bana. Wannan shi ne yayin da 65 kacal na irin wannan laifi aka yi rajista a daidai wannan lokacin na bara.

A sa'i daya kuma, wannan jami'in 'yan sandan birnin London ya fayyace cewa tun farkon rikicin Falasdinu, an kama mutane 75 dangane da laifukan da aka ambata.

A wannan asabar ne aka gudanar da zanga-zanga mafi girma a birnin London na nuna goyon bayan al'ummar Gaza da kuma yin Allah wadai da laifukan gwamnatin sahyoniyawa.

 

4178392

 

 

 

 

captcha