IQNA

Jagoran Katolika na duniya: Hare-Hare kan Gaza ta'addanci ne

21:56 - November 30, 2023
Lambar Labari: 3490230
Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya bayyana hare-haren soji da gwamnatin Sahayoniya ta yi a yankin Zirin Gaza a matsayin harin ta'addanci.

Jaridar Washington Post ta Amurka ta bayar da rahoton a ranar Alhamis cewa: A karshen watan Oktoba, an jefa bama-bamai, da tankokin yaki da ta kutsa cikin Gaza, shugaban gwamnatin Sahayoniya, Isaac Herzog, ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho da Paparoma Francis.

Jaridar Washington Post ta bayyana cewa, a cikin wannan tattaunawa, Paparoma Francis ya bayyana hare-haren soji da gwamnatin Sahayoniya ta yi a yankin Zirin Gaza a matsayin ta'addanci.

A cewar jaridar, Herzog ya nuna adawa da kalaman Paparoman, yayin da Paparoman ya ci gaba da cewa: “Wajibi ne a hukunta wadanda ke da alhakin abin da ke faruwa, amma hakan bai shafi farar hula ba.

Jaridar Washington Post ta rubuta cewa: A baya Paparoma ya jaddada a wani taron jama'a cewa rigingimun Gaza sun wuce yaki kuma wannan ta'addanci ne.

Ita dai wannan jarida ta Amurka ta kara da cewa: Kalaman da Fafaroma ya yi a bainar jama'a game da ayyukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun harzuka kungiyoyin da ke goyon bayan Isra'ila irinsu kwamitin yahudawan Amurka da kuma tada zaune tsaye tsakanin shugabannin Yahudawa da fadar Vatican.

 

 

 

4185054

 

captcha