IQNA

Karatun shahidin Falasdinu mai dadi yana bayyana haduwa da Allah

19:30 - December 31, 2023
Lambar Labari: 3490397
IQNA - Bidiyon karatun mujahid na dakarun Qassam wanda ya haddace kur'ani baki daya kuma ya samu raunuka ya kuma yi shahada a cikin sujada a kwanakin baya a wani harin da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai a zirin Gaza ya samu karbuwa daga masu amfani da suka karanta. ayoyin da ke bayanin lokacin mutuwa da haduwa da Allah.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Qassam Tissir Abu Taymeh wani Bafalasdine na bataliyar Qassam wanda kuma shi ne limamin masallacin kuma mai karatun kur’ani ya samu rauni kuma ya yi shahada a yayin da ya yi sujada a harin da Isra’ila ta kai a yankin zirin Gaza kwanakin baya.

A yau an buga audio na Qassam Tissir Abu Taymeh yana karatun ayoyin suratu Mubaraka Juma a shafukan sada zumunta, kuma yana bayanin halin da yake ciki a lokacin shahadarsa.

Dakika 38 na wannan karatun yana bayani ne kan halin da wannan shahidi Bafalasdine yake ciki a daidai lokacin da suke ganawa da Allah.

A cikin wannan faifan bidiyo Qassam Tissir Abu Taymeh malamin kur'ani kuma mayaka dan gwagwarmayar Falasdinu yana karanta aya ta 6 zuwa ta 8 a cikin suratul Mubaraka Juma da armashi.​

 

 
 

 

 

 

captcha