IQNA

Karatun ayoyin Suratul Haqqa tare da Sayed Karim Mousavi

14:50 - January 16, 2024
Lambar Labari: 3490486
IQNA - Sayyid Karim Mousavi, fitaccen makaranci daga Iran , ya karanta suratul Haqqa a wani taro a kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tare da gudanar da zagayowar ranar shahadar Janar Qassem Soleimani da kuma bisa al’adar shekaru 3 da suka gabata an shirya da gudanar da jerin tarurruka da kur’ani mai tsarki a kasar Iraki.

A bana an gudanar da wadannan da'irar ne daga ranar 3 zuwa 13 ga watan Janairu a kasar Iraki tare da halartar manyan makaratun kasashen duniya da na Iran. Cibiyar kur'ani ta Basaer Al-Qur'aniyyah da Al-Ittihad da Al-Tamagamat Al-Qur'aniyyah na kasar Iraki ne suka shirya wadannan da'ira.

Daga cikin masu karatu da haddar da suka halarta a wadannan da'irar akwai Sayyid Karim Mousavi, fitaccen malami makarancin kur’ani na Iran,  wanda ya gabatar da shirye-shirye a garuruwa daban-daban na kasar Iraki.

A cikin shirin za a ji karatun Seyyed Karim Musawi na aya ta 18 zuwa 22 a cikin suratul Haqqa.

 

https://iqna.ir/fa/news/4193996

​​

Abubuwan Da Ya Shafa: karatu makaranci kur’ani shahada kasar iraki
captcha