Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yeni Shafaq cewa, hoton shahid Hazem Haniyeh yana karanta ayoyin suratu Mubaraka Ibrahim (a.s) a daya daga cikin masallatan Gaza, ya samu karbuwa daga masu amfani da shafukan sada zumunta.
A cikin wannan faifan bidiyo shahid Hazem Haniyeh dan Ismail Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinawa (Hamas) yana karanta wadannan ayoyi na suratu Mubaraka Ibrahim cikin murya da murya mai dadi.
Shahid Hazem Haniyeh tare da ‘yan uwansa biyu Amir da Mohammad da kuma wasu ‘yan uwa da dama sun yi shahada a ranar Larabar da ta gabata, daidai da Sallar Idi, a wani hari da mayakan yahudawan sahyoniyawan suka kai kan motar da ke dauke da su.