Janye wannan mataki dai ya zo ne sakamakon irin matakan da kungiyoyin kare hakkin bil adama da na musulmi suka dauka domin kalu balantar lamarin wanda ya yi hannu riga da dokokin kasar.
Yanzu haka dai dalibar ta koma ta ci gaba da karatu kamar yadda ta saba tare da saka hijabinta ba tare da wata masaa ba, duk kuwa da cewa lamarin ya faru ne ba tare da tsammani ba, domin kuwa ba a taba yi wa wani hakan ba awanan cibiya sai ita.
Musulmi a kasar Spain dais u ne kimanin kasha cikin dari na na mutanen kasa da yawansu ya kai 46.5, kuma suna gudanar da harkokinsu a cikin ‘yanci a kasar wadda ta zama daya daga cikin kasashe da ke karkashin musulmi a tarihi.
Dalibar ta bayyana cewa ta yi farin ciki matuka dangane da yadda aka dauke wannan doka da aka kafa mata a wannan cibiya.
Kungiyar kae hakkin bil adama ta SOS ta taka gagarumar rawa wajen ganin cewa ta kwato ma wannan daliba hakkinta da aka tauye mata, inda ta shigar da kara a ranar 8 ga wannan wata na Satumba, kuma daga karshe dai aka yi nasara kan wannan batu.