Ministan yawon bude ido na kasar Indonesia ya bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta dauki kwararan matakai dangane da wasanni na kwamfuta da ke tozarta dakin Ka'abah mai alfarma.
A zantawarsa da tashar CNN, Ministan yawon bude ido na kasar Indonesia Sandiaga Uno ya bayyana cewa, irin wadannan wasanni na kasashe-kashe suna da bababr illa ga yara, sannan kuma yanzu lamarin ya fara shafar abubuwa masu tsarki na addini, wanda a cewarsa ba za su amince da haka a cikin kasarsu.
A nasa bangaren ma'aikatar leken asiri ta kasar Indonesia ya ce, ma'aikatarsa tana yin aiki tare da jami'an 'yan sanda, domin bin diddigin wadanda suke harhada wadannan wasanni na yanar gizo a cikin Indonesia domin kama su.
A cikin wasannin an fortnite dai ana nuna kashe-kashe da yake-yake, wanda kuma daga baya ana nuna yadda ake kai hari kan dakin Ka'abah da kashe mutane a cikin masallacin harami mai alfarma.
Akwai mutane fiye da miliyan 350 da suke yin wannan wasa a fadin duniya a halin yanzu.